Birtaniya

Rikicin Birtaniya yana da nasaba da siyasa, inji Cameron

masu kwasar ganima sanadiyar rikicin birtaniya a yankin Birmingham
masu kwasar ganima sanadiyar rikicin birtaniya a yankin Birmingham REUTERS/Darren Staples

Prime Ministan Birtaniya David Cameron yace rikicin da ke ci gaba da bazuwa a sassan yankunan birtaniya yana da nasaba da matsalar rikicin siyasa.Rehotanni daga Britaniya na nuna cewar, har yanzu ana cigaba da samun yaduwar tashin hankalin a wasu sassan yankunan kasar, duk da kara yawan jami’an tsaro.A yanzu haka dai an samu tashin hankalin a garuruwan Manchester, da Salford, da Liverpool, da Wolverhampton, da Nottingham, da Leicester da kuma Birmingham, yayin da ake saran Majalisar kasar zata koma aiki gobe, dan nazarin halin da ake ciki.