Birtaniya

‘Yan sanda sun kama mutane 600 da laifi a rikicin Birtaniya

'yan sandan Birtaniya na kokarin kwantar da tanzoma
'yan sandan Birtaniya na kokarin kwantar da tanzoma (REUTERS)

‘Yan sandan Birtaniya sun ce sun kama mutane kusan 600 da laifin haddasa tanzoma da kwasar ganima a rikicin da aka kwashe kwanaki ana gudanarwa a cikin kasar.A yanzu haka dai sama da mutane Dubu daya ne ‘Yan sandan suka cafke, yayin da kotunan Birmingham da Manchester suka fara sauraren karar daruruwan mutanen da ake zargi.Rikicin kasar dai ya haddasa hasara da dama a cikin kasar, inda aka balle daruruwan shaguna tare da cinna wa gidaje wuta. Mutane da dama dai sun rasa rayukansu sanadiyar rikicin da ya barke a ranar Assabar.