Faransa

Faransa tace tattalin arzikinta baya cikin matsala

Ministan kudin Faransa François Baroin
Ministan kudin Faransa François Baroin RFI Hausa

Yayin da shugaban Bankin Duniya ke gargadi kan tattalin arzikin duniya, kasar Faransa tace tattalin arzikinta na nan da karfin sa.Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake bukatar Faransa da Jamus su bada tallafi don magance matsalolin da kasashen Italy da Spain ke fuskanta.Masana tattalin arzikin duniya suna ganin bayar da tallafin ya zama wajibi domin magance matsalar da tattalin arzikin duniya ke ciki, musamman kasashen yammaci da tattalin arzikinsu ya shiga tsaka mai wuya. 

Talla

Saurari kalaman Masani Tattalin Arziki Hon Sama’ila Muhammed

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.