Birtaniya

David Cameron ya nemi a gyara tarbiyyar yara

Prime Ministan Birtaniya David Cameron
Prime Ministan Birtaniya David Cameron REUTERS/Olivia Harris

PM kasar Birtaniya David Cameron ya ce gyara tarbiyar al’umar kasar zai baiwa mahimci, bayan tashe tashen hankulan matasa.Ya fadi haka yayin ziyarar mazabarsa dake tsakiyar Ingila, inda ya ce ‘yn kasar Britaniya sun san menene ba daidai ba, amma abunda tambaya shine suna da karfin zuciyar gyarawa. suna da zuciyar gyara lalacewar al’umar kasar ta Britaniya, na rashin daukan nauyi, son kai, nuna rashin damuwa da halin da wasu ke ciki, yaran da basu da iyaye, makarantun da babu tarbiya, bada garabasa ba tare da aiki ba, laifi babu hukunci, hakki babu daukan nauyi, da al’umar da babu tsawatarwa.