Isa ga babban shafi
FARANSA

Akwai Shakku a ci gaba da Sauraren karar Jacques Chirac na Faransa

Tsohon Shugaban kasar Faransa Jacques Chirac
Tsohon Shugaban kasar Faransa Jacques Chirac AFP
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau

A kasar Faransa ana Shakkun sake ci gaba da sauraren karar tsohon Shugaban kasar Jacques Chirac da ake zargi yin almubazzaranci da dukiyar kasa bayan wani rehoto da ke cewa tsohon shugaban na fama da rashin lafiya.Jacques Chirac mai shekaru 78 na haihuwa shi ne shugaban Faransa na farko da ya fuskanci Shari’a tun bayan yakin Duniya na biyu. Sai dai kuma shugaban ya bukaci ci gaba da sauraren karar amma Lauyansan ya wakilce shi.Shugaban wanda ya yi suna a duniya bayan nuna adawarsa ga yakin Amurka a Iraqi a shekarar 2003, ana zarginsa ne da fatali da kudin Jama’a da Cin hanci da Rashawa bayan tallafawa Jam’iyyarsa a lokacin da yake yakin neman zabensa a shekarar 1995.Akwai dai yiyuwar Idan har aka kama shugaban da laifi, za’a yanke masa hukuncin dauri shekaru 10 a gidan yari tare da biyan kudin tara $10,000.Ana dai sa ran Alkali mai Shari’a Dominique Pauthe zai yanke hukunci dangane da rehoton rashin lafiyar Shugaban domin dage sauraren karar zuwa wani lokaci. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.