Ukrain

Kotu ta yankewa Tymoshenko daurin shekarru 7

Tsohuwar Prime Ministar  Ukrain Yulia Tymoshenko tare da Lauyanta
Tsohuwar Prime Ministar Ukrain Yulia Tymoshenko tare da Lauyanta REUTERS/Gleb Garanich

Wata kotu a kasar Ukraine, ta yanke hukunci daurin shekaru 7ga Tsohuwar Prime Minista kasar Ukrain, Yulia Tymoshenko, kan laifin  sanya kasar tafka asarar Dala miliyan 200, wajen cinikin gas da kasar Russia.Kungiyar kasashen Turai da Amurka, sun yi watsi da zargin, inda suke danganta shi da siyasa, kuma ana ganin matakin na iya tarnaki kan bukatar Ukraine na shiga kungiyar kasashen Turai.