Faransa

Fafatawar ‘yan takarar Jam’iyyar Socialist a Faransa

fafatawa tsakanin Martine Aubry da  François Hollande
fafatawa tsakanin Martine Aubry da François Hollande PATRICK KOVARIK / AFP

‘Yan Takarar neman shugabancin kasar Faransa, a Jam’iyar gurguzu ta Socialists, Francois Holande, da Martin Aubry, jiya sun sake fafatawa a mahawarar da aka gudanar ta kafar telabijin, a yakin neman zabensu kafin zaben raba gardamar da za’a gudanar a karshen mako.Aubry ta zargi Hollande, da cewar bai taba rike wani babban mukami ba, ko da minista ne, da zai bashi damar kwarewar mulki, yayin da Hollande yace shi fatansa, shi ne hada kan ‘Yan Jam’iyya domin kawo karshen shugabancin shugaba Sarkozy.