Spain

An rage darajar karfin biyan bashin Spain

Fira Ministan Spain Jose Luis Rodriguez Zapatero
Fira Ministan Spain Jose Luis Rodriguez Zapatero © REUTERS

Standard and Poors da ke auna karfin biyan basukan kasashe ya rage darajar kasar Spain wajen karfin biyan basukan da ke kanta bayan faduwar darajar manyan bankunan Spain.Standard & Poors yace matsalar rashin aikin yi da matsalar tattalin arzikin kasashen Turai shi ya haifar da wannan koma baya ga SpainYanzu haka kuma Spain ta rage yawan kudaden da take kashewa domin tabbatar da matakin tsuke bakin aljihu don farfado da darajar tattalin arzikin kasar