FARANSA

Hollande ya lashe zaben fitar-da-gwani a Jam’iyyar Socialist ta faransa

Francois Hollande, na Jam'iyyar Gurguzu ta Socialist a Faransa
Francois Hollande, na Jam'iyyar Gurguzu ta Socialist a Faransa @Reuters

Francois Hollande ya lashe zaben fitar-da-gwani na jam’iyyar Gurguzu ta Socialist a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a badi a kasar Faransa, bayan ya doke abokiyar karawar shi Martine Aubry da rinjayen kuri’u kashi 56.Mista Hollande ya nemi hadin kan ‘ya’yan Jam’iyyar Socialist domin fuskantar kalubalen da ke gabansu, inda ya sha alwashin kalubalantar Shugaba Nicolas Sarkozy.Shugaba Sarkozy wanda ake tunanin zai nemi tazarce a zaben mai zuwa, wani sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a na nuni da cewa Shugaban zai sha kaye a zaben sakamakon da ya ba Hollande nasara.Tuni kuma Martine Aubry ta bayyana goyon bayanta ga Hollande domin cim ma gurinsu na kawo karshen mulkin Sarkozy a Faransa.