EU

Tarayyar Turai zata gudanar da taron gaggawa

Angela Merkel ta Jamus tare da  Nicolas Sarkozy na Faransa.
Angela Merkel ta Jamus tare da Nicolas Sarkozy na Faransa. AFP / Jean-Christophe Verhaegen

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai zasu gudanar da wani taron gaggawa a Brussels domin tattauna tsarin da zasu bi wajen kawo karshen matsalar tattalin da ya shafe su.Akwai dai fargabar matsalar tattalin arzikin kasar Girka zai iya shafar kasashen Italiya da Spain.An bukaci kasar Italiya ta gabatar da sabon tsarin tattalin arzikinta kafin bude taron a yau Laraba.A kasar Jamus akwai kuri’ar amincewa da Angela Merkel ke bukata daga majalisar kasar domin Karin kudaden tallafin ceto darajar EURO kafin halartar Taron.