Faransa

Strauss-khan yasa gidansa kasuwa a Woshington

Dominque Strauss-Kahn lokacin da yake amsa tambayoyi a kafar Telebijin
Dominque Strauss-Kahn lokacin da yake amsa tambayoyi a kafar Telebijin Reuters/Francois Guillot

Tsohon Shugaban Hukumar Bada lamuni ta Duniya, Dominique Strauss Kahn, yasa gidansa kasuwa da ke birnin Washington, watanni biyar bayan kama shi, da zargin yunkurin fyade.Mista Kahn da matarsa zasu sayar da gidansu ne akan Dala miliyan biyar da dubu dari biyu, sabanin yadda suka saya akan kudi Dala miliyan hudu a shekarar 2007.