Ingila

Kotu ta yi watsi da bukatar Assange na Wikileaks

Julian Assange, shugaban shafin tonon asiri na WikiLeaks
Julian Assange, shugaban shafin tonon asiri na WikiLeaks REUTERS/Andrew Winning

Wata kotu a birtaniya ta yanke hukuncin mika Julian Assange a kotun Sweden domin amsa tamboyin zargin fyade da ake masa bayan ya daukaka kara.Hukuncin wanda aka yanke a yau laraba, mai shari’a John Thomas yace Mista Assange zai gurfana a gaban kotun Sweden inda ake zarginsa da yiwa wata mata fyade a birnin Stockhom a bara.Tuni Mista Assange ya musanta zargin da ake masa, inda ya danganta zargin ga wandanda ke adawa da ayyukan shafinsa na Wikileaks da ke tonon asirin kasashen duniya da hukumomi.Har yanzu dai ba a san ko Mista Assange wanda ya kwashe tsawon shekara daya ana tsare da shi a cikin gida ko zai iya daukaka kara a kotun kolin Birtaniya ba.