Italiya

Majalisar Italiya zata kada kuri’ar amincewa da matakin tsuke bakin aljihu

Shugaban Jam'iyyar Democrat Pier Luigi Bersani, lokacin da yake jawabi a zauren majalisa
Shugaban Jam'iyyar Democrat Pier Luigi Bersani, lokacin da yake jawabi a zauren majalisa Reuters/Tony Gentile

A yau Juma’a ne majalisar kasar Italiya zata kada kuri’ar amincewa da matakin tsuke bakin aljihun gwamnati kamar yadda Tarayyar Turai suka bukata domin kaucewa matsalar tattalin arzikin da ke addabar kasashen, inda kuma ake jiran kafa sabuwar gwamnati domin kawo karshen Mulkin Berlusconi.Za’a gabatar da muhawara tsakanin wakilan Majalisar bayan da kwamitin kasafin kudin a babban majalisar kasar ya amince da matakin a jiya alhamis.Ana sa ran tsohon kwamishinan kasashen Turai Mario Monti shi zai gaji Fira Minista SilVio Berlusconi.Berlusconi wanda ya sha kaye a majalisar a ranar Talata, ya sha alwashin yin murabus bayan an kada kuri’ar dokar daurewar hada hadar kudaden Italiya a zauren majalisun kasar guda biyu.