EU

Turai zata yi fama da matsalar tattalin arziki a badi

Kwamishinan mai kula da tattalin arzikin kasashen Turai Olli Rehn.
Kwamishinan mai kula da tattalin arzikin kasashen Turai Olli Rehn. REUTERS/Thierry Roge

Kungiyar Kasashen Turai ta yi hasashen cewa za’a samu matsalar komadar tattalin arzikin Turai a badi bisa halin matsalolin dimbin bashi wasu kasashen yankin da ya kai ga wasu shugabannin kasashen rasa kujerunsu.A cewar Olli Rehn, Kwamishina mai kula da tattalin arzikin Turai, yace tattalin arzikin Turai na tsaye ne, yanzu haka, kuma akwai fargabar yadda lamarin zai kasance nan gaba.Saboda fargabar ko kasar Italiya zata iya sauke dimbin bashin dake wuyanta, Olli Rehn ya bukaci kasar Faransa, kasa ta biyu wajen karfin tattalin arziki a yankin data kara daukar Karin matakan tabbatar da dorewar tattalin arzikinta, wajen zabtare wasu kasafi marassa tasiri.Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya kaddamar da tsarin tada komadan tattalin arziki, kuma ya tsaya kai da fata cewa komi na bisa kai’da.Matsalar tsarin tattalin arzikin kasar Italiya ya yi kokarin yin gaba da rawanin Fira Ministan kasar Silvio Berlusconi wanda da bakinsa ya bayyana yin Murabus.Shugaban kasar Amirka Barak Obama na daga cikin wadanda suka kira Shugaban Italiya Giorgio Napolitano domin nuna goyon baya game da matakan siyasa dana tattalin arziki.