Mali

'Yan bindiga sun sace Faransawa 2 a Mali

Sojojin kasar Mali da ke aiki a arewacin kasar
Sojojin kasar Mali da ke aiki a arewacin kasar © Serge Daniel/RFI

Rahotanni daga Bamako na kasar Mali na cewa an sace wasu masu aikin agaji ‘yan kasar Faransa 2, suna zaman-zamansu a wani Otel dake kauyen Hombori.Bayanai na nuna cewa wasu dauke da bindigogi suka sace mutanen.Sau 6 kenan ‘yan bindiga na sace Faransawa a yankin Sahel, inda ake danganta sace-sacen da cewa aikin ‘yan kungiyar Al-Qaeda ne.