EU

Batun Iran zai mamaye taron ministocin Turai

William Hague, Ministan harakokin wajen Birtaniya
William Hague, Ministan harakokin wajen Birtaniya REUTERS/Ramzi Boudina

Batun daukar mataki kan kasar Iran shi zai mamaye Taron Ministocin kasashen Turai da za’a gudanar yau Alhamis, inda wakilan kasashen zasu tattauna yadda zasu dauki mataki ga rehoton Majalisar Dinkin Duniya kan shirin kasar Iran na makamashin Nukiliya.  

Talla

Kasar Iran tun da farko ta musanta rehoton inda tace shirinta na Nukiliya na zaman lafiya ne ba zai cutar da kowa ba.

Birtaniya dai zata nemi sake kakubawa kasar Iran takunkumi bayan farma ofishin jekadancinta a birnin Tehran.

A jiya laraba ne gwamnatin Birtaniya ta bayyana janye jami’an Diflomasiyarta daga kasar Iran tare da rufe ofishin jekadancin Iran a birnin London domin maar da martani ga abin day a faru a Tehran.

Yanzu haka wasu manyan kasashen Turai da suka hada da kasar Faransa da Jamus da Holland da Norway sun janye jakadunsu daga Iran.

‘Yan kasar Iran sun farma ofishin jekadancin Birtaniya ne bayan matakin da kasar ta dauka na sake kakubawa kasar Takunkumi da katse duk wata hulda tsakaninta da Iran.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI