EU

An kasa cim ma matsaya a taron kasashen Turai don ceto euro

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, a Taron kokarin ceto tattalin arzikin kasashen Turai a birnin Marseille
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, a Taron kokarin ceto tattalin arzikin kasashen Turai a birnin Marseille Reuters/Jean-Paul Pelissier

Kokarin da kasashen Faransa da Jamus suka yi domin ganin sauran kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da sabuwar yarjejeniyar da suka gabatar don magance matsalar tattalin arzikin kasashen ya cutura.

Talla

Bayan kwashe lokaci ana muhawara a birnin Brussels, shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yace kasashe 17 masu amfani da kudin euro zasu bi wasu dabaru daban maimakon neman amincewar sauran kasashen kungiyar.

Kasar Faransa da Jamus suna ta kokarin matsin lamba domin kaddamar da tsauraran matakan ga kasafin kudaden kasashen.

Amma kuma Fira Ministan birtaniya David Cameron yace sabuwar yarjejeniyar bata cikin bukatar kasar Birtaniya.

After nearly 10 hours of talks between EU leaders, Mr Sarkozy said he would have preferred a new treaty involving all 27 member states.

Bayan kwashe sa’o’i kusan goma ana tabka muhawara, Mista Sarkozy yace ya dace Mambobin kasashen 27 su amince da sabuwar yarjejeniyar. Amma kuma a cewarsa Fira ministan Birtaniya ya gabatar da wasu bukatu da zasu ba birtaniya damar gudanar da sauye-sauye.

Yanzu haka Fira Ministan Birtaniya, David Cameron yace zai yi duk abinda ya dace domin kare bukatun kasarsa a zauren taron.

A cewarsa abin bukata ga Birtaniya a samu daidaituwar kudaden euro, kodayake yace ba zasu amince da duk wani abinda zai sabawa Birtaniya ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI