Rasha

PM Rassia Putin ya yi watsi da suka kan zaben 'yan Majalisu

PM Rasha Vladimir Putin
PM Rasha Vladimir Putin REUTERS/Alexsey Druginyn/RIA Novosti/Pool

PM Kasar Rusha Vladimir Putin, ta hannun wani mai magana da yawun sa ya ce duk da korafe-korafen da aka yi ta nunawa, game da zabukan majalisar Wakilan kasar, babu wani abinda za ayi, domin bakin alkalami ya bushe.

Talla

Mai Magana da yawun PM, mai suna Dmitry Peskov, ya ce koda za'a baiwa masu korafe-korafen dakkan kuri'un da suke ja game da su, babu wani abinda zai sauya.

Wannan na biyo bayan umarni ne da Shugaban kasar ta Rasha Dmitry Medvedev ya bayar cewa jami'an zabe su duba koken magudi da ka gabatar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI