Italiya

Mutane 17 suka hallaka sakamakon hadarin jirgin ruwan shkatawa

REUTERS/Tony Gentile

Masu aikin ceto sun gano gawar wata mata cikin jirgin ruwan shakatawan Costa Concordia na kasar Italiya da yayi hadari, abunda ya kawo mamatan zuwa 17.

Talla

An samu gawar cikin jirgin wanda ya kife da fasinjoji fiye da 4,000 ranar 13 ga wannan wata na Janairu. Har yanzu akwia sauran mutane 15 da suka bace bayan hadarin kuma ake ci gaba da neam.

Za a shafe kimanin makonni hudu da kafin kawo karshen aiyukan gano sauran mutanen dake cikin jirgin ruwan shakatawan kasar ta Italiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI