Sweden

Wani Mutum ya tsira da ransa bayan kankara ta lullube shi tsawon watanni biyu

Motar da aka gani kankara ta lullube ta a arewacin Umea  arewacin kasar Sweden kuma an isko mutumin da kae yanye da motar da ransa bayan kwashe tsawon watanni biyu.
Motar da aka gani kankara ta lullube ta a arewacin Umea arewacin kasar Sweden kuma an isko mutumin da kae yanye da motar da ransa bayan kwashe tsawon watanni biyu. REUTERS/Rolf Hojer/Scanpix

Hukumomin Kasar Sweden sun fara gudanar da bincike game da yadda dusar kankara ta lullube wani mutum mai suna Peter Skylberg tsawon watanni biyu, ba tare da an gano shi ba.

Talla

Rahotanni sun ce, mutumin mai shekaru 44, an gano shi ne a wani daji, cikin motarsa, da kankarar ta sa ya kafe, kuma ta lullube shi tun watan a Disemban bara, kafin ranar juma’a a makon jiya da gano shi.

Bayanai sun ce, lokacin da motar ta kafe, yana dauke da abinci, abinda ya taimake shi, da kuma ruwan kankara da ya yi ta sha.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.