Australia

Rudd zai kalubalanci Gillard a Australia

Tsohon Fira Ministan kasar Australia Kevin Rudd, ya bayyana aniyar shi ta sake yin takarar mukamin shugabancin jama’iyya mai mulkin kasar, inda zai kalubalanci Julia Gillard mai ci yanzu , a zaben da za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa.

Kevin Rudd Tsohon Fira minsitan Australia
Kevin Rudd Tsohon Fira minsitan Australia REUTERS/Yuriko Nakao/Files
Talla

Tsohon Shugaban jama’iyyar Labour, wanda Gillard ta kada a zaben da aka yi a shekarar 2010, ya ajiye mukamin shi na ministan harkokin wajen kasar a ranar laraba, don shiryawa zaben.

Yayin da yake Magana a birnin Washigton na kasar Amurka, Mista Rudd yace Julia ta gagara rike amanar da al’ummar Autralia suka danka mata, don haka zai kalubanace ta don dawo da wannan amanar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI