Belgium-Switzerland

Ana zaman makoki a kasar Belgium

Daruruwan mutane suna juyayin mutuwar wadanda suka mutu sanadiyar hadarin mota a Belgium
Daruruwan mutane suna juyayin mutuwar wadanda suka mutu sanadiyar hadarin mota a Belgium REUTERS/Yves Herman

Ana gudanar da zaman makoki cikin kasar Belgium, sakamakon mutuwar mutane 28 a hadarin motar safa da ke kan hanyar zuwa Switzerlands. Mutane 22 daga cikin wadanda suka hallaka yara ne, kuma akwai mutane 52 yayin da motar ta yi hadari, kuma sauran mutane 24 sun tsira da raunika.

Talla

Masu gabatar da kara na binciken musabbabin hadari, amma sun ce matukin motar yana tafiya cikin tsanaki lokacin da aka samu hadarin.

Shugaban kasar Switzerland Evelyn Widmer-Schlumpf da takwaransa fira ministan kasar Belgium Elio Di Rupo, sun mika sakon ta’aziyarsu ga ‘iyalan wadanda suka mutu sanadiyar hadarin motar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.