Faransa

Dan bindigan Faransa ya mutu

Wani Hoton Bidiyo na Mohammed Merah da aka samu yana tukin mota.
Wani Hoton Bidiyo na Mohammed Merah da aka samu yana tukin mota. © France 24

Jami’an tsaro a kasar Faransa sun tabbatar da mutuwar dan bindigar da ya kaddamar da kashe kashe a Toulouse wanda suka bayyana da sunan Muhammed Merah mai shekaru 23 na haihuwa bayan ‘Yan Sandan sun kwashe kwanaki biyu suna farautar shi a wani gida da ya ke buya.

Talla

Sai dai babu cikakken bayani game da gawar shi amma ‘yan Sandan sun ce ya mutu sanadiyar samamen da  suka kaddamar a gidan da yake buya.

‘Yan sanda uku ne suka mutu daya daga cikinsu kuma ya samu rauni a samamen da suka gudanar a Toulouse.

An kiyasta jin amon albarussai kimain 300 a lokacin da ‘Yan sandan ke farautar dan bindigar.

Muhammed Merah ya yi ikirarin harba harsashen bindiga da ya kashe mutane Tara da suka kunshi ‘Yayan Yahudawa uku. Tare da bayyana kaddamar da hare hare a matsayin daukar fansan kisan da Isra’ila ke wa Falesdinawa.

Muhammed Merah ya yi ikirarin shi dan kungiyar Al Qaeda ne wanda ya samu horo a yankin Wziristan da ke kan iyaka da Pakistan da Afghanistan.

Har yanzu dai babu gawar shi da aka bayyana fili bayan ‘Yan Sandan Faransa sun yi ikirarin kashe shi domin tabbatar da asalin shi da kuma akidar shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.