Bosnia

Amnesty ta bukaci yin adalci ga matan da aka yi wa Fyade

Matan Musulmin kasar Bosnia suna kuka a lokacin da za'a yi Jana'izar wadanda aka kashe a Srebrenica da dakarun Sebia suka kashe Musulmi 8,000
Matan Musulmin kasar Bosnia suna kuka a lokacin da za'a yi Jana'izar wadanda aka kashe a Srebrenica da dakarun Sebia suka kashe Musulmi 8,000 REUTERS/Dado Ruvic

Kungiyar kare hakkin da Adam ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin kasar Bosnia domin tabbatar da yin adalci ga Matan da aka yi wa fyade da wadanda aka azabtar, a lokacin yakin da aka gwabza a kasar a shekarar 1990.

Talla

Kungiyar tace har yanzu ba a gurfanar da wadanda suka yi aikata Fyadan ba, yayin da daruruwan matan da al’amarin ya rutsa da su, suke cikin mummunan hali, ba tare da kulawa da lafiyar su ba.

Kungiyar tace duk da alkawarin da hukumonin birni Sarayebo suka yi a shekarar 2010, domin kula da wadanda lamarin ya shafa, har yanzu ba wani abu da ya biyo baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.