Faransa-Senegal

Sarkozy da Sall sun kulla yarjejeniyar tsaro da tallafi ga Senegal

Nicolas Sarkozy  a lokacin da yake karbar bakuncin Macky Sall a fadar Shugaban kasa.
Nicolas Sarkozy a lokacin da yake karbar bakuncin Macky Sall a fadar Shugaban kasa. REUTERS/Benoit Tessier

Gwamnatin kasar Faransa ta kulla yarjejeniyar tsaro da tallafi da kasar Senegal bayan ganawar Macky Sall da Sarkozy a birnin Paris. Sall ya yi alkawalin gudanar da shugabanci nagari tare da neman inganta hulda tsakanin Faransa da kasashen Afrika.

Talla

A jiya Laraba ne Macky Sally ya gana da Sarkozy wanda ke neman sake zabensa wa’adi na biyu a zaben Faransa. Shugabannin biyu sun gana a fadar shugaban kasa tare da cin abinci tare.

Tun da farko dai akwai yarjejeniyar tsaro tsakanin Senegal da Faransa da kasashen biyu suka kulla a shekarar 2008. Akwai kuma yarjejeniyar rage dakarun Faransa a Senegal daga 1,200 zuwa 300 da sarkozy ya kulla da Abdulaye Wade a shekarar 2010.

Ministocin harakokin wajen kasashen biyu ne suka saka hannu a yarjejeniyar tallafin kudi euro Miliyan 130 da Faransa zata ba Senegal.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.