Isa ga babban shafi
Birtaniya

An cafke wani Dan Jarida a Birtaniya saboda zargin Cin Hanci

Jaridu da Mujallu a wajen sayarwa
Jaridu da Mujallu a wajen sayarwa Wikimedia Commons
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed
Minti 1

‘Yan sanda a Birtaniya sun Cafke wani Editan shahararriyar Jaridan The Sun, saboda zargin shi da bai wa ma’aikatan gwamnati toshiyar baki. Jami’an tsaron sun cafke Duncan Larcombe, a gidan shi da ke Kent a kudancin Ingila, tare da cafke wasu tsoffin Jami’an tsaro Biyu Mace da Namiji, a gidan su da ke Lancashire.

Talla

Sai dai dukkaninsu an bada su Beli har zuwa watan Yuli kamar yadda ‘Yan Sandan kasar suka bayyana.

Ana zargin dan jaridan da hada baki wajen bayar da toshiyar baki, da aikata ba daidai ba a aikin gwamnati.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.