France-zaben shugaban kasa

Shugabar jam’iya mai ra’ayin rikau ta kasar Fransa FN tace ba za ta zabi kowa ba a zagaye na 2 na zaben shugabancin kasar Fransa.

1 мая 2012 г. Париж. Лидер крайне-правого Национального фронта Марин Ле Пен выступает перед своими сторонниками на площади Оперы
1 мая 2012 г. Париж. Лидер крайне-правого Национального фронта Марин Ле Пен выступает перед своими сторонниками на площади Оперы REUTERS/Charles Platiau

Bayan da ta zo ta uku a zagaye na farko na zaben shugabancin kasar Fransa. Uwargida Marine Le Pen taki ta raba gardama har zuwa wannan rana ta 1 ga watan mayu, kan wanda zata goyawa baya tsakanin Nicolas Sarkozy da Francois Hollande.Sai ma kira ta yi ga magoya bayanta da cewa, suna da yancin su zabi son ransu, a zaben da za a gudanar zagaye na biyu a ranar 6 ga wannan watan mayu, tare da cewa, su jefa farar kuri’a ta yan baruwanmu a zaben da za’a yi zagaye na 2.