Faransa

Sarkozy da Hollande zasu tabka Muhawara amma Le Pen tace banza zata kada wa kuri’arta

hoton da aka hada François Hollande yana murmushi  Nicolas Sarkozy yana jawabi a  à Dijon,
hoton da aka hada François Hollande yana murmushi Nicolas Sarkozy yana jawabi a à Dijon, Reuters/Montage RFI

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy zai fukskanci kalubale a muhawar da za’a gudanar ta Kafar Telebijin a yau Laraba daga abokin hamayyar shi Francois Hollande na Jam’iyyar gurguzu ta socialist da aka yi hasashen zai lashe zaben shugaban kasa a zagaye na biyu.

Talla

Da Misalin karfe 7:00 na yamma agogon GMT ne ‘Yan takarar biyu zasu tabka muhawara domin gamsar da Faransawa akan Manufofinsu.

A wani gangami da Marine Le Pen ta hada a jiya Talata, ‘Yar takarar shugaban kasar da ta zo matsayi na uku a zagayen Farko, ta yi kaca-kaca da manufofin Hollande da Sarkozy, tare da alkawalin ba zata kada masu kuri’a ba, kuma magoya bayanta da dama sun ce kuri’arsu zata je ga banza.

A ranar 6 ga watan Mayu ne Faransawa zasu zabi shugaban kasa tsakanin Sarkozy da Hollande a zagaye na biyu.

Le Pen ita ce ‘Yar takarar da ta zo ta Uku a zagayen Farko da yawan kuri’u kashi 17.9 don haka ne Sarkozy da hollande suka shiga farautar magoya bayanta domin kada masu kuria a zagaye na biyu.

Le Pen ta la’anci manufofin Hollande da Sarkozy inda tace ‘Yan barandan Bankin Turai ne.

Sarkozy dai ya dade yana fatan ganin ranar da zai tunkari abokin hamayyar shi Hollande, tun bayan da ya sha kaye a zagayen farko, Sarkozy ya bukaci gudanar da Muhawara sau uku domin wayar da kan Faransawa game da fanufofin shi tare da kalubalantar Hollande.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.