Zaben Faransa

Sharhin Jaridun Faransa a yau

Wasu Jaridun kasar Faransa
Wasu Jaridun kasar Faransa

Hankalin Jaidun Faransa a yau ya rabu gida biyu domin wasu sun mayar da hankali ne akan yakin neman zaben ‘Yan siyasa da aka gudanar a jiya ranar bukin ma’aikata, wasu kuma jaridun sun mayar da hankali ne akan muhawarar da za’a gudanar a yau tsakanin Sarkozy da Hollande a kafar Telebijin.

Talla

Jaridar L’Humanite da Le Figaro su ne jaridun da suka yi waiwayen gangamin siyasar da aka gudanar a jiya Talata amma bayanan Jaridun ya sha ban-ban.

Jaridar Le Figaro tace Sarkozy ya hada gangamim magoya baya 100,000 a tsakiyar Birnin Paris inda ya yi kira ga kungiyoyin kwadago su yi watsi da gangaminsu don bin tawagar ci gaban Faransa.

A nata bangaren Jaridar L’Humanite tace kungiyoyin kwadago sun hada ganagamim mutane 750,000 dauke da tutoci da ke nuna adawa da Shugaba Sarkozy.

Wasu jaridun kuma a Faransa sun ce Hollande da Sarkozy sun shirya hanyoyin da zasu tunkari juna a Muhawarar da za’a gudanar a yau Laraba.

Aujourd'hui en France ta zayyana karfin ‘Yan takarar guda biyu da kuma rauninsu da kalubalen da kowannensu zai fuskanta. Amma Jaridar tace Hollande zai ba Sarkozy mamaki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.