Turai-Guinee Bissau

kungiyar tarayyar turai ta ce zata kakabawa sojojin da suka kifar da gwamnatin kasar Guine Bissau takunkumi

Kunghiyar Tarayyar Turai ta kakabawa Jagororin juyin mulki na kasar Guinea Bissau takunkumin hana su sukuni, bayaga jerin takunkumin da Kungiyar kasashen yammacin Africa suka riga suka kakaba masu.Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai, ta haramtawa Sojojin kasar ta Guinea tsoma kafarsa cikin nahiyar Turai, sannan kuma dukkan kaddarorinsu an karbe.Kungiyar tace za’a gabatar da sunayen wadannan sojoji gobe.