Faransa

Sarkozy da Hollande sun tabka muhawara tare da sukar juna

Dandalin Muhawarar da aka gudanar tsakanin Hollande da Sarkozy
Dandalin Muhawarar da aka gudanar tsakanin Hollande da Sarkozy RFI

Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, da abokin adawarsa, Francois Hollande, sun yi musayar kalamai marasa dadi a mahawarar karshe da suka gudanar yammcin jiya, kafin zabe zagaye na biyu a karshen mako. ‘Yan takarar guda biyu sun tabka muhawara akan batutuwa da dama da suka hada da tsare tsaren tattalin arziki da kuma tsarin shige da fice. 

Talla

Sarkozy ya kare rawar da gwamnatinsa ta taka a cikin shekaru biyar, tare da kokarin ceto Faransa daga fadawa matsalar tattalin arziki, amma Hollande yace yanzu haka kasar na fuskantar mawuyacin hali, ta fannin tattalin arziki. Nan take ne Sarkozy ya kira Hollande makaryaci.

Mliyoyan Faransawa ne suka kalli muhawarar da aka gudanar ta kafar Telebijin inda ‘Yan takarar suka fuskanci juna.

Hollande wanda ya bude muhawar ya zargi Sarkozy da raba al’ummar Faransawa tare da kiran a zabe shi domin zai kasance shugaba mai adalci.

Amma Sarkozy ya mayar da martani inda ya yaba da kalaman Hollande a matsayin Sukar da ba hujja. Sarkozy yace ya samar da sabbin tsare tsare da suka shafi tsarin kudin Fensho ba tare da Faransawa sun fito sun yi zanga-zanga ba.

‘Yan takarar guda biyu sun zargi juna wajen bayar da bayanan da ba gaskiya ba akan batun tattalin arziki da tsarin shige da fice da samar da aikin yi ga al’umma.

Da farko dai Sarkozy ya fuskanci kalubale akan batun tattalin arziki inda shugaban yace babu adalci idan aka zarge shi akan matsalar tattalin arzikin Faransa bayan kwashe shekaru kasar na fuskantar barazana daga shugabannin da ya gada.

Masana dai sun ce Sarkozy ya kware a wajen Muhawara kuma akan haka ne ya nemi gudanar da muhawar sau uku tsakanin shi da Hollande amma muhawarar da aka gudanar a jiya ita ce ta farko kuma ta karshe kafin zaben a ranar 6 ga watan Mayu.

Sarkozy ya zargi tsarin tattalin arzikin da Hollande yace zai yi amfani da shi inda ya kalubalanci alkawalin Hollande na kokarin samar da aikin yi 60,000 ga Faransawa.

Sarkozy yace matakin zai jefa Faransa cikin dimbim bashi.

Sannan Sarkozy ya zargi tsarin harajin Holande inda yace tsarin zai taimakawa masu hannu da shuni.

Sai dai ‘Yan takarar guda biyu dukkaninsu suna da manufa guda akan batun Musulunci, domin Hollande yace idan aka zabe shi zai ci gaba da aiwatar da dokar nan ta haramta wa Mata sa hijabi (Burqa) a kasar Faransa.

Amma Sarkozy ya yi kokarin fito da hanyoyin da zai gurgunta abokin adawar shi wanda ya lashe zagaye na farko. Kuma zaben ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna Sarkozy zai sha kaye a zagaye na biyu.

A ranar Lahadi Al’ummar Faransa zasu kada kuri’a, amma ‘Yan takarar guda biyu suna kokarin ganin yadda zasu samu goyon bayan Marine Le Pen da magoya bayanta kodayake ‘Yar takarar da ta zo na uku a zagayen farko tace banza zata kadawa kuri’arta domin manufofin ‘yan takarar sun saba wa Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.