Rasha

Rasha ta amince a yi zanga-zanga jajibirin rantsar da Putin

Shugaban Rasha, Dmitry Medvedev da  Vladimir Poutine da  Pyotr Biryukov a birnin Moscow lokacin bukin ranar ma'aikata
Shugaban Rasha, Dmitry Medvedev da Vladimir Poutine da Pyotr Biryukov a birnin Moscow lokacin bukin ranar ma'aikata REUTERS/Dmitry Astakhov/RIA Novosti/Kremlin

Hukumomin kasar Rasha, a karon farko sun bada dama ga ‘yan adawa domin gudanar da gangami a tsakiyar birnin Moscow. Wannan kuma na zuwa ne kwana daya kamin kaddamar da shugaba Vladmir Putin a wa’adi na uku.  

Talla

Masu gangamin zasu yi jerin gwano na tsawon kilomita guda da rabi akan kogin Moscow, kafin daga bisani su taru a dandalin Bolatnaya.

Wannan zanga-zangar dai ita ce mafi girma da zata girgiza Rasha tun a farkon shekara 1990, domin mayar da martani ga zaben ‘yan majalisun kasar da aka yi.

Amma yawan masu zanga-zangar na raguwa da sauri sakamakon yadda farinjinin Putin ya karu a zaben ranar 4 ga watan Maris, kuma sabbin kungiyoyi suna ta ci gaba da fito da dabarun shimfida sabuwar rayuwa.

Amma wasu daga cikin Karin ‘yan tawayen kasar na kokarin gudanar da gangamin da ba bisa ka’ida ba, domin kalubalantar Vladmir Putin.

Ana dai saran cewar zasu iya tara miliyoyin mutane, a yayinda ‘Yan kasar Moscow ke himmar tara makudan kudade domin gangamin ya yi armishi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.