Faransa

Hollande ne sabon shugaban Faransa bayan ya kada Sarkozy

François Hollande Sabon shugaban kasar Faransa wanda ya kada Nicolas Sarkozy
François Hollande Sabon shugaban kasar Faransa wanda ya kada Nicolas Sarkozy REUTERS/Philippe Wojazer

Dan takarar Jam’iyyar Gurguzu ta Socialist François Hollande ya kada shugaban kasa mai ci Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasar Faransa zagaye na biyu. Hollande shi ne Mutum na Farko da ya lashe zaben shugaban kasa karkashin Jam’iyyar Gurguzu tun zamanin François Mitterrand a shekarar 1988.

Talla

A Zagaye na Biyu an samu kashi 81 na mutanen da suka fito kada kuri’a. Hollande ya samu nasarar zagaye na biyu da rinjayen kuri’u kashi 51.67. Sarkozy kuma ya samu kashi 48.33.

A lokacin da Hollande ya ke gabatar da Jawabin samun nasarar zaben shi, Sabon shugaban yace zai kasance shugaban Faransawa ba tare banbanci ba. “Faransa ba zata rabu ba, inji Hollande a lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Shugabannin Kasashen Turai da dama sun Kira Hollande ta wayar Salula domin taya shi murna, wanda su ke ganin zaben shi zai taimaka wajen warware matsalar tattalin arziki.

A lokacin yakin neman zaben Hollande, yace akwai hanyoyin magance matsalar tattalin arzikin Turai ba lalle sai ta hanyar matakan tsuke bakin aljihu ba.

Tuni dai Shugaban Amurka Barack Obama ya mika sakon gayyatar Hollande zuwa fadar White House a wannan watan bayan taya shi murnar lashe zabe.

A lokacin yakin neman Zaben Shi, Hollande ya samu goyon bayan wasu Turawan Jamus bayan kalubalantar shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel da ke jaddada tsaurara matakan tsuke bakin aljihun gwamnatocin kasashen Turai.

Angela Merkel dai ta nuna goyon bayanta ga Nicolas Sarkozy domin lashe zaben shugaban kasa.

Sai dai bayan fitar da sakamakon zabe, Gwamnatin Jamus tace zata yi aiki da Gwamnatin Hollande domin warware matsalar tattalin arziki.

Tuni dai Angela Merkel ta kira Hollande ta wayar Salula domin taya shi murna tare da gayyatar shi don tattaunawa a birnin Berlin.

Yanzu haka dai kasuwannin hannayen jarin kasashen Asiya sun fadi saboda rashin tabbas akan makomar tattalin arziki bayan shan kayen Sarkozy a Faransa.

Nicolas Sarkozy ya taka muhimiyyar rawa tare da Angela Merkel wajen kokarin warware matsalar tattalin arzikin da ya shafi kasashen Turai, sai dai sun fuskanci kalubalae game da manufarsu ta tsaurara matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da ya janyo zanga-zanga a wasu kasashen Turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.