Girka-EU-IMF

Girka zata yi watsi da matakan tsuke bakin Aljihun Gwamnati

Alexis Tsipras Dan Jam'iyyar Syriza  a kasar Girka
Alexis Tsipras Dan Jam'iyyar Syriza a kasar Girka Reuters

Shugaban Jam’iyyar Syriza ta kasar Girka, Alexis Tsipras, ya yi alkawarin soke tallafin kasashen Turai da Hukumar bada Lamuni ta Duniya tare da yin watsi da shirin tsuke bakin aljihu idan ya kafa Gwamnati. Yanzu haka Jam’iyyar Syriza ta fara tattaunawa da sauran Jam’iyyu domin kafa gwamnatin hadin gwiwa.

Talla

Tsipras da Jam’iyar sa ta zo ta biyu a zaben kasar, yace tuni ‘Yan kasar Girka suka soke yarjejeniyar bashin, bayan kawar da Gwamnatin da ta karbo shi.

Ana saran ya cim ma yarjejeniyar kafa gwamnatin cikin kwanaki uku, kuma ya shaidawa jam’iyyun da ke shirin hada kai da shi, su janye duk wani goyan bayansu akan shirin tsuke bakin aljihun Gwamnati.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.