Fransa

Fra Ministan Fransa Francois Fillon ya gabatar da murabus din gwamnatinsa

Le Premier ministre français François Fillon le 23 avril 2012.
Le Premier ministre français François Fillon le 23 avril 2012. Reuters/Yves Herman

A yau alhamis Fra Ministan kasar Fransa Francois Fillon ya gabatar da murabus din gwamnatinsa, wace zata ci gaba da tafiyar da wasu muhimman ayuka kafin zababben shugaban kasar Francois Hollande ya fara aiki a ranar talata mai zuwa, inda zai nada wata sabuwar gwamnati.Mr Fillon ya mika wasikar Murabus din gwamnatinsa ne ta hannun wani jami’in tsaron jamhuriya, wanda shi kuma zai isar da ita ga shugaban kasar mai barin gado Nicolas Sarkozy.Murabus din Mr Fillo da ya kasance Fra Minista daya tak, da shugaba Sarkozy ya yi a shekaru 5 na wa’adin mulkinsa, ta zo ne kwana guda bayan gudanar da zaman taron majalisar ministocin gwamnatinsa na karshe da aka yi a jiya laraba a fadar shugaban kasar.Haka kuma ta zo ne jim kadan bayan da kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta tabbatar da sahihancin sakamakon zaben shugabancin kasar ta Fransa, na ranar lahadin da ta gabata.