Rasha-Amurka

Obama ya taya Putin murnar sake zama shugaban Rasha

Shugaban Rasha Vladmir Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin Reuters

Ta Wayar Salula, Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya taya shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin murnar sake zama shugaba a karo na uku, bayan kwashe lokaci shugabannin biyu suna adawa da juna. Sai dai Putin yace ba zai samu damar halartar taron kasashen G8 da za’a gudanar a Amurka.

Talla

Fadar Kremlin tace, shugabanin biyu sun tattaunawa ta wayar Salula, akan yadda zasu bunkasa dangantaka a tsakanin kasashensu.

Mista Putin ya dade yana zargin Amurka da biyan masu zanga zanga kudade a kasar, tun bayan tanzomar da ta barke bayan kammala zaben ‘Yan Majalisu.

Putin ya shaidawa Obama ba zai samu damar halartar Taron kasashe Takwas masu karfin tattalin arziki ba saboda kokarin kafa sabuwar gwamnati a kasar Rasha.

Ana sa ran shugabannin biyu zasu hadu a taron kasashen G20 da za’a gudanar a Mexico a watan Yuni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.