Sharhin Jaridu

Sharhin jaridun duniya

Jaridar Punch: (Najeriya)Gwanatin jihar Legas jiya tace a shirye ta ke ta koma kan teburin tattaunawa, da likitocin da ta kora a shekaran jiya.Kwamishinan kiwon lafiya na jihar ne, wato Dokta Jide Idris, ya gayawa yan jarida jiya a Legas, ya na mai cewa dole ne yasa gwamnatin ta kori likitocin.Idan dai ba’a manta ba gwamnan jihar, Babatunde Fashola, ya kori likitoci kusan dubu daya domin yajin aikin da su ka shiga don neman karin albashi.Sai dai wannan tayin da aka musu bai sa sun janye wata kara da lilkitocin su ka shigar a Kotun ma’aikata da ke Legas tun gabanin koresu.DIRECT NIGER (NIGER) (kamfanin dillancin labarai)Wani mutum ya kashe kansa a yayin da ya cinnawa kansa wuta a kasar Niger.Shi dai marigayin, mai suna Ma’azu Soumaila a ranar da ya kashe kansa, abokanan aikinsa sun ganshi rike da jarka cike da petir wanda hakan ya bawa kowa mamaki.A cewar kampanin dillancin labaran, da Ma’azu ya shiga wajen aikin nasa, an ganshi ya zagaya ofis sannan ya shiga cikin wani daki ya kulle kansa ya kuma cinnawa kansa wuta.Duk kokarin da yan kwana – kwana da abokan aikinsa su ka yi wajen ceto shi, sai da Ma’azu ya halaka domin wutar ta riga ta cinyeshi.Kuma an rasa abin da ya sa ya aikata wannan danyen aiki.A cewar gidan dillancin labaran, shi marigayin mutm ne shuru-shuru kuma mai addini.Irin wanna lamari dai bai taba faruwa a kasar ta Niger ba, mafi akasari ya fi faruwa ne a kasashen Asia.(Dala lamai in Tibet) AMINIYA (NAJERIYA)Wata likitan hakori a kasar Poland mai suna Anna Mackowiak (34) za ta fuskanci zaman gidan yari har na tsawon shekaru uku bayan an same ta da laifin cirewa tsohon suarayinta hakoransa gaba daya.Ita dai likitan sun bata da tshohon saurayin nata ne mai suna, Marek Oslzwiski kuma dan shekara 45, yan kwanakin kadan da su ka wuce.Shi dai Marek ya je asibitin da tsohuwar budurwar tasa ke aiki ne inda ya kai kukan ciwon hakori.Ita kuma Anna sai ta ce ya kwanta za ta duba hakorin nasa inda ta mai allurar kashe zafi ta banbare duk hakoran nasa ba tare da sanin sa ba.A yayin da ake tuhumarta, Anna ta ce ta yi kokarin ta kai zuciyarta nesa dan ta gudanar da aikin amma abin ya cutura sai da zuciyarta ta sa ta cire ma tsohon saurayin na ta hakoransa duka saboda fushin rabuwar da su ka yi.