Turai

Kungiyar tarayyar Turai zata dauki wani sabon matakin ladabtarwa kan kasar Syriya

A ranar litanin mai zuwa ne, kungiyar tarayyar Turai zata dauki wani sabon matakin ladabtarwa kan kasar Syriya, tare da karbe kaddarorin wasu kamfanoni 2, da kuma wasu mutane 3 wadanda ake ganin suna tallafawa gwamnatin Bashar al-Assad da kudade, kamar yadda majiyar diflomasiyar kungiyar ta sanar a yau juma’a.Majiyar ta bayyana cewa, dama dai akwai yarjejeniya tsakanin kasashen kungiyar ta tarayyar turai 27, wajen daukar matakan ladabtarwa kan kasar ta Syriya, wanda a wannan karo shine na 15 da suka zartar a kanta, tun bayan barkewar rikicin siyasar kasar yau sama da shekara guda da ta gabata