Faransa

Hollande ya karbi ragamar shugabancin Faransa

Sabon Shugaban Faransa François Hollande tare da Nicolas Sarkozy mai barin gado a fadar Elysee
Sabon Shugaban Faransa François Hollande tare da Nicolas Sarkozy mai barin gado a fadar Elysee REUTERS/Jacky Naegelen

Mai ra’ayin gurguzu, Francois Hollande ya karbi ranstuwar shugabancin Faransa tare da bayyana fatar samar da sauyi a kasar da Nahiyar Turai. Ana sa ran Sabon shugaban zai zabi Fira Ministan kafin ya nufi zuwa kasar Jamus don tattaunawa da Angela Merkel.

Talla

Bayan Rantsar da Hollande, sa’o’I kalilan ne zai nufi Jamus a ziyararsa ta farko a matsayin shugaban Faransa domin tattaunawa da shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel.

Ana dai sa ran Francois Hollande zai zabi Jean-Marc Ayrault matsayin Fira Minista wanda shi ne shugaban'ya'yan jam’iyyar gurguzu a zauren majalisa.

Francois Hollande, shi ne shugaban Faransa na farko daga jama’iyyar Gurguzu cikin shekaru 20, kuma sabon shugaban ya sha alwashin kawo sauye sauye masu muhimmanci a Faransa.

Wasu daga cikin alkawurran da Mista Hollande ya yi sun hada da karin haraji ga masu hannu da shuni.

Sabon Shugaban yace zai sauya yadda faransa ke dangantaka da sauran kasashen duniya, musamman abin da ya shafi yake yaken da ta shiga a baya, don haka ne ma sabon shugaban ya yi alkawarin janyen sojojin Faransa daga Afghanistan kafin karshen shekarar 2012, Matakin da Shugaban Hamid Karzai ya yi marhaban da shi.

Sai dai kuma Sabon shugaban yana da manufar ci gaba da haramta saka Hijabi a Faransa kamar yadda ya bayyana a lokacin da yake muhara tsakanin shi da Sarkozy wanda ya kafa dokar a Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.