Faransa

Sarkozy ya zama tsohon shugaban kasar Faransa

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy REUTERS/Yves Herman

Yanzu Haka Nicolas Sarkozy, ya zama tsohon shugaban kasar Faransa, bayan rantsar da Hollande abinda ya kawo karshen mulkinsa na shekaru biyar da ‘Yan Faransa da dama suka yi ta korafi akai.

Talla

Nicolas Sarkozy ya sauka daga karagar mulki a matsayin daya daga cikin shugabanni wadanda basu da farin jini a tarihin Faransa. Kuma Sarkozy shi ne shugaba na biyu a tarihin kasar da ya sha kaye a neman wa’adi na biyu.

Sarkozy wanda yace zai fice daga siyasa da zaran ya fadi zabe, yaki ganawa da manema labarai tun bayan shan kashin da ya yi, sabanin lokacin da ya hau mulki, inda yake lale da manema labarai.

Farin jinin Sarkozy ya fara samun koma baya ne, sakamakon kasa cika alkawuran da ya yi wa ‘Yan kasar na kawo sauyi, da kuma shirinsa na kara shekarun ritaya daga aiki, da rage harajin attajirai.

‘Yan Faransa sun zargi shugaban da kasa magance cin hanci da rashawa, da rashin aikin yi, inda ya kai kashi 10, da kuma zargin karbar kudaden yakin neman zabe daga attajira Lilian Betancourt, da Tsohon shugaban kasar Libya, Muammar Ghadafi.

Duk da farin jinin da ya samu wajen kawo karshen yaki Rusha da Georgia, farin jinin Sarkozy ya sake faduwa sanadiyar mayar da kasar kungiyar NATO, da kuma tura sojin kasar zuwa Afghanistan, tare da shiga sahun gaba wajen jagorantar yakin kasar Libya.

Akan haka ne ‘Yan Faransa ba suyi kasa a gwiwa ba, wajen nuna masa fushinsu lokacin zaben kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.