Hollande ya zabi Ministocin da zasu yi aiki tare a Faransa
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An fitar da jerin sunayen Ministocin gwamnatin François Hollande da suka hada da Pierre Moscovici a matsayin Ministan kudi da Laurent Fabius a matsayin sabon Ministan harakokin wajen Faransa. Kuma rabin Ministocin duka mata ne kamar yadda Hollande ya yi alkwali a yakin neman zaben shi.
Ministocin sun kunshi mutane 34 bayan zaben Fira Minista Jean-Marc Ayrault.
Christiane Taubira, ita ce aka zaba Ministan Shari’a babban Mukamin Minista a kasar Faransa.
Sauran Ministocin mata da zasu yi aiki da Hollande sun kunshi Marisol Touraine, a matsayin Ministan Lafiya, sai Cecile Duflot matsayin Ministan gidaje da kuma sauran matan da suka taimakawa Hollande a yakin neman zaben shi da suka hada da Aurelie Filipetti, da aka ba mukamin Ministan Al’adu da kuma Najat Vallaud-Belkacem matsayin Ministan ‘Yancin Mata.
A yau Alhamis da Misalin kafe 1:00 agogon GMT Sabbin Ministoci zasu fara ganawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu