Girka

Akwai alamun sake gudanar da zabe a Girka

Wani taron shugabannin Jam'iyyun Siyasar kasar Girka
Wani taron shugabannin Jam'iyyun Siyasar kasar Girka EUTERS/Louisa Gouliamaki/Pool

Kasar Girka ta kama hanyar zuwa wani sabon zaben ‘Yan Majalisu, saboda yunkurin kafa gwamnati ya ci tura, tsakanin Jam’iyyun siyasar kasar. Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, tace duk kokarin da suka yi na samun hada kai domin kafa gwamnati ya ci tura.

Talla

Ana saran sake komawa fagen zabe a ranar 17 ga watan gobe, inda Jam’iyun kasar zasu sake fafatawa tsakanin masu goyan bayan tsuke bakin aljihun gwamnati da tallafin kasashen Turai, da kuma wadanda ke neman ganin an yi watsi da shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.