Amurka-Faransa

Strauss-Kahn ya shigar da kara domin kalubalantar Nafisatou Diallo

Tsohon shugaban hukumar bada Lamuni ta duniya Dominique Strauss-Kahn
Tsohon shugaban hukumar bada Lamuni ta duniya Dominique Strauss-Kahn Reuters/Gonzalo Fuentes

Tsohon Shugaban Hukumar Bada lamuni ta Duniya, Dominique Strauss Kahn, ya shigar da kara a kotu inda yake bukatar Nafisatou Diallo, matar da ta yi masa zargin yunkurin yi mata fyade a New York, ta biya shi Dala miliyan guda, saboda bata masa suna.

Talla

Strauss-Khan ya shigar da kara ne ranar Litini, inda yace kazafin da ta matar ta yi masa, ya bata masa suna tare da cin zarafin sa, saboda haka yake bukatar shiga tsakanin kotu saboda biyan shi diyya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.