EU-Faransa

Faransa ba zata sanya hannu ga yarjejeniyar kasafin kudaden kasashen Turai ba

Pierre Moscovici. Sabon Ministan kudin Faransa
Pierre Moscovici. Sabon Ministan kudin Faransa RFI

Gwamnatin Kasar Faransa, tace ba zata sanya hanun kan yarjejeniyar kasafin kudaden kassahen Turai ba, a wani mataki da ya fito da sabanin da ke tsakanin sabuwar gwamnatin kasar, da kungiyar kasashen Turai.

Talla

Sabon Ministan kudin Faransa, Pierre Moscovici, ya sanar da matsayin kasar, inda yake cewa babu yadda zasu amince da yarjejeniyar a yadda take yanzu, dole sai an kara wata shadara da zata nuna hanyoyin ci gaba.

Ministan yace, aikin da ke gaban gwamnatinsu, shi ne magance basusukan jama’a da rage gibin kasafin kudi da kuma shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar.

Moscovici yace, duk wata kasa da ke amfani da bashi wajen tafiyar da aikace aikacen ta, to lalle zata talauce.

Kasashen Turai dai sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar da zata rage gibin kasafin kudi, da kuma tabbatar da cewar kowacce kasa tana aiwatar da shirin, abinda ya sanya daukar matakin tsuke bakin aljihu a wasu kasashe, al’amarin day a haifar da haifar da zanga zanga.

Tun kafin zaben kasar, shugaba Francoise Hollande, yace idan an zabe shi, zai sake duba yarjejeniyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.