Birtaniya-Turai

PM kasar Burtaniya David Cameron ya nemi kasashen turai masu kashe kudin Yuro da su kula da zumuncinsu

PM kasar Britania David Cameron ya sake kira ga Shugabannin kasashen dake amfani da kudaden Euro dasu dauki kwararan matakai, domin kare sukurkucewar zumuncinsu sakamakon dimbin basukan da kasar Girka ke fama dashi.Da yake jawabi a birnin Manchester David Cameron ya bukaci kasashen masu amfani da kudin Euro su 17, duk da cewa Britaniya bata cikinsu, dasu yi la’akari da irin wawukeken gibin da ake samu wajen kashe kudade.