Girka

Za’a sake gudanar da zabe a kasar Girka

Mambobin gwamnatin rikon kwaryar Grika a lokacin da ake rantsar dasu a fadar shugaban kasaa Athens
Mambobin gwamnatin rikon kwaryar Grika a lokacin da ake rantsar dasu a fadar shugaban kasaa Athens REUTERS/John Kolesidis

An rantsar da Panagiotis Pikrammenos, matsayin shugaban rikon kwarya a kasar girka wanda zai jagoranci kasar har zuwa kammala zabe a ranar 17 ga watan Yuni. A yau Alhamis ne za’a rantsar da ministocinsa 16.

Talla

A ranar 17 ga watan Yuni ne, ‘Yan kasar Girka za su koma runfunan zabe a karo na biyu, don sake sabon zabe, a dai dai lokacin da ake ci gaba da bayyana fargaba kan makomar kasar a tsakanin kasashe masu anfani da kudin euro.

Yanzu shugaban riko Panagiotis Pikrammenos, zai ci gaba da jagorantar gwamnatin tare da shirya sabon zabe, bayan gudanar da wani a ranar Shida ga watan Mayu. An dogara da zaben ne domin samar da gwamantin da za ta aiwatar da tsare tsaren da asususn lamuni na Duniya IMF da kungiyar taraiyyar Turai EU, suka tsara wa kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.