Birtaniya-Scotland

Al-Megrahi ya mutu, Maharin lockerbie

Maharin jirgin saman lockerbie  Abdelbaset Ali Mohmet al-Megrahi wanda ya mutu yana da shekaru 60
Maharin jirgin saman lockerbie Abdelbaset Ali Mohmet al-Megrahi wanda ya mutu yana da shekaru 60 (Photo : Reuters)

Abdelbaset Ali Mohmet al-Megrahi, ya Rasu, mutumin da aka samu da tayar da Bam wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 270 a shekarar 1988. A yau Litinin ne za’a binne shi bayan ya mutu sanadiyar cutar Cancer.

Talla

Abdelbaset al- Megrahi ya rasu ne a jiya Lahadi misalin karfe 1:00 na rana. in ji kaninshi Abdelhakim al- Megrahi.

Shi dai marigayin ya rasu ne yana dan shekaru 60 a duniya bayan ya sha fama da ciwon daji,

A watan jiya ne dan uwansa, Abdelhakim al- Megrahi ya yi ikrarin cewa kwanakin al Megrahi kirgaggu ne ganin yadda ciwon na shi ya yi tsanani.

A shekarar 2001, wata kotu a kasar Scotland ta yanke wa al-Megrahi hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 27 domin irin rawar da aka zarge shi ya taka a fashewar jirgin Lockerbie, amma an sako shi a shekarar 2009, bayan likitoci sun tabbatar ba zai wuce watanni uku a raye ba. Wanda hakan bai wa kasar Birtaniya dadi ba.

Al Megrahi a lokacin da ya ke da rai, ya dade yana bayyana cewa ba shi da hannu akan fashewar jirgin wanda ya tarwatse a sararin samaniyar garin Lockerbie da ke kasar Scotland.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.