Jamus-Girka

gwamnatin Jamus ta musanta zargin cewa Waziriyar kasar ta nemi gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a a kasar Girka

La chancelière allemande Angela Merkel se dit prête à accueillir François Hollande «les bras ouverts», 7 mai 2012 à Berlin.
La chancelière allemande Angela Merkel se dit prête à accueillir François Hollande «les bras ouverts», 7 mai 2012 à Berlin. REUTERS/Fabrizio Bensch

Kakakin Waziriyar Jamus Angela Marekel da kakkausar murya ya sake karyata zargin cewa, waziriyar ta gabatar da shawarar gudanar da kura’ar jin ra’ayin jama’a kan ci gaba da amfani da kudin Euro a kasar Girkakakakin ya bayyana cewa, waziriyar bata hurumin tsoma bakinta a cikin harakokin siyasar cikin gida kan matsalar tattalin arzikin kasar Girka.A lokacin wani taron manema labarai da gwamnatin Jamus ke gudanarwa, Kakakin M Georg Streiter ya bayyana cewa, wannan magana karya ce tsagwaronta, domin Uwargida Markel bata taba bada shawarar gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a a kasar Girka ta wannan fanni ba, ko kuma ta wata siga makamanciyar haka.