France-France24-rfi

ministan al'adu da yada labaran Fransa ta soke maganar hade Radio Fransa da tashar Talabijin ta France24 waje daya

Aurélie Filippetti, la nueva ministra de Cultura.
Aurélie Filippetti, la nueva ministra de Cultura. Reuters

Sabuwar ministan raya Al’adun da sadarwa ta kasar Fransa Aurelie Filippetti a yau litanin ya bayyana dalilan da suka sa aka dakatar da hadewar tashar Radio France Internationale da tashar Talabijin ta France 24.Inda tace a lokacin yakin neman zaben shugabancin kasar na jam’iyar socialiste kafin a zabe shi shugaban kasar, Fransa Francois Hollande ya taba saka hannu kan takardun koken nanu a dawa da wannan gamin gabizar Radiyo Fransa da tashar talabijin ta France 24 dake watsa shirye shiryensu a kasashen ketare.Uwargida Filippetti ta kara da cewa, zasu dauki dukkanin matakan da suka dace, wajen ganin Radiyo Fransa ya ci gaba da yada shirye shiryensa dai dai yadda ya saba, musaman ga nahiyar Afrika, inda yake da Dimbin masu saurare dake bukatar samun labarai na gaskiya ba tare da nuku nuku ba.