Faransa-Girka

Akwai yiyuwar yaduwar bashi a Turai idan Girka ta fice euro, inji Moscovici

Pierre Moscovici. Sabon Ministan kudin Faransa
Pierre Moscovici. Sabon Ministan kudin Faransa Reuters

Ministan kudin Faransa Pierre Moscovici ya yi gargadin cewa idan kasar Girka ta fice daga kungiyar kasashe masu amfani da kudin EURO, akwai yiwuwar yaduwar matsalar bashi a yankin. Sai dai Moscovici ya ce Faransa zata yi iya kokarinta na ganin hakan ba ta faru ba.

Talla

Ministan kudin ya kuma ce, yana da yakinin kasashen Faransa da Jamus za su cim ma matsaya ga jerin shawarwari da hukumomin birnin Paris suka mika na hanyoyin da za’a ceto tattalin arzikin Turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.